Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -

Zabura 76 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Zabura 76
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Tare da kayan kiɗi masu tsirkiya. Zabura ta Asaf. Waƙa ce.

1 A cikin Yahuda an san Allah; sunansa da girma yake a cikin Isra’ila.

2 Tentinsa yana a Salem mazauninsa yana a Sihiyona.

3 A can ya kakkarya kibiyoyin wuta, garkuwoyi da takuban, makaman yaƙi. Sela

4 Darajarka tana da haske, fiye da darajar tuddai waɗanda suke cike da namun jeji masu yawa.

5 Jarumawa sun zube kamar ganima sun yi barcinsu na ƙarshe; ba ko jarumi guda da zai iya ɗaga hannuwansa.

6 A tsawatawarka, ya Allah na Yaƙub, doki da keken yaƙi suka kwanta ba motsi.

7 Kai kaɗai ne za a ji tsoro. Wane ne zai iya tsayawa sa’ad da ka yi fushi?

8 Daga sama ka yi shelar hukunci, ƙasa kuwa ta ji tsoro ta kuwa yi tsit,

9 sa’ad da kai, ya Allah, ka tashi don ka yi shari’a, don ka cece dukan masu shan wahala a ƙasar. Sela

10 Tabbatacce fushinka a kan mutane kan jawo maka yabo, waɗanda suka tsira daga fushinka za su zama kamar rawaninka.

11 Ku yi alkawari wa Ubangiji Allahnku ku kuma cika su; bari dukan ƙasashen maƙwabta su kawo kyautai ga Wannan da za a ji tsoro.

12 Ya kakkarya ƙarfin masu mulki; sarakunan duniya suna tsoronsa.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:



ကြော်ငြာတွေ