Zabura 65 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 65 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Wata waƙa. 1 Yabo ya dace da kai, ya Allah, a Sihiyona; a gare ka za mu cika alkawuranmu 2 Ya kai wanda yake jin addu’a a gare ka dukan mutane za su zo. 3 Sa’ad da zunubai suka sha ƙarfinmu, ka gafarta laifofinmu. 4 Masu albarka ne waɗanda ka zaɓa ka kawo kusa don su zauna a filayenka! Mun cika da abubuwa masu kyau na gidanka, na haikalinka mai tsarki. 5 Ka amsa mana da ayyuka masu banmamaki na adalci, Ya Allah Mai Cetonmu, begen dukan iyakar duniya da kuma na tekuna masu nesa, 6 wanda ya yi duwatsu ta wurin ikonka, bayan ka kintsa kanka da ƙarfi, 7 wanda ya kwantar da rurin tekuna, rurin raƙumansu, da kuma tumbatsar al’ummai. 8 Waɗanda suke zama can da nesa sukan ji tsoron manyan ayyukanka; inda safe ke haskaka yamma kuma ta shuɗe kakan sa a yi waƙoƙin farin ciki. 9 Kana kula da ƙasa kana kuma yi mata banruwa; kana azurta ta a yalwace. Rafuffukan Allah sun cika da ruwa don su ba mutane hatsi, don haka ne ka ƙaddara. 10 Ka kwarara ta da ruwa ka kuma baje kunyoyinta; ka sa ta yi laushi da yayyafi ka kuma albarkaci tsire-tsirenta. 11 Saboda alherinka, ya Allah, an sami kaka mai albarka, amalankenka kuwa sun cika har suna zuba. 12 Makiyayan hamada sun cika har suna zuba; tuddai sun rufu da murna. 13 Wurin dausayin kiwo sun rufu da garkuna kwari kuma sun cika da hatsi; suna sowa don farin ciki. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.