Zabura 46 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 46 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta ’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. 1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala. 2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku, 3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. Sela 4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama. 5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe. 6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke. 7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela 8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya. 9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta. 10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.” 11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. Sela |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.