Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -

Zabura 30 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Zabura 30
Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda.

1 Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.

2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.

3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami.

4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki.

5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.

6 Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.”

7 Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro.

8 A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.

9 “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka?

10 Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”

11 Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,

12 don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:



ကြော်ငြာတွေ