Zabura 150 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 150 1 Yabi Ubangiji. Yabi Allah a cikin wurinsa mai tsarki; yabe shi a cikin sammai na ikonsa. 2 Yabe shi saboda ayyukansa masu iko; yabe shi saboda mafificin girmansa. 3 Yabe shi da ƙarar kakaki, yabe shi da garaya da molo, 4 yabe shi da ganga kuna taka rawa, yabe shi da kayan kiɗi na tsirkiya kuna kuma busa, 5 yabe shi da kuge mai ƙara, yabe shi da kuge masu ƙara sosai. 6 Bari kowane abu mai numfashi yă yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.