Zabura 137 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 137 1 A bakin kogunan Babilon muka zauna muka yi kuka sa’ad da muka tuna da Sihiyona. 2 A can a kan rassan itatuwa muka rataye garayunmu, 3 gama a can masu kamunmu suka sa mu yi waƙoƙi, masu ba mu azaba suka nema waƙoƙin farin ciki; suka ce, “Ku rera mana ɗaya daga cikin waƙoƙin Sihiyona!” 4 Yaya za mu rera waƙoƙin Ubangiji a baƙuwar ƙasa? 5 In na manta da ke, ya Urushalima, bari hannuna na dama manta da iyawarsa. 6 Bari harshena yă manne wa rufin bakina in ban tuna da ke ba, in ban so Urushalima farin cikin mafi girma ba. 7 Ka tuna, ya Ubangiji, abin da mutanen Edom suka yi a ranar da Urushalima ta fāɗi. Suka yi ihu suka ce, “A ragargaza ta, A ragargaza ta har tushenta!” 8 Ya Diyar Babilon, an ƙaddara ke zuwa hallaka, mai farin ciki ne wanda ya sāka miki saboda abin da kika yi mana, 9 shi da ya ƙwace jariranki ya fyaɗa su a kan duwatsu. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.