Zabura 123 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 123 Waƙar haurawa. 1 Na tā da idanuna gare ka, gare ka da kursiyinka yake cikin sama. 2 Kamar yadda idanun bayi suna duban hannun maigidansu, kamar yadda idanun baiwa suna duban hannun uwargijiyarta, haka idanunmu suna duban Ubangiji Allahnmu, sai ya nuna mana jinƙansa. 3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, gama mun jimre da reni mai yawa. 4 Mun jimre da wulaƙanci daga masu girman kai, reni mai yawa daga masu fariya. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.