Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -

Zabura 12 - Sabon Rai Don Kowa 2020


Zabura 12
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda.

1 Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.

2 Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya; zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce suna cike da ruɗu a zukatansu.

3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu da kuma kowane harshe mai fariya,

4 masu cewa, “Da harsunanmu za mu yi nasara; leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”

5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata, zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji. “Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”

6 Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure, kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu, aka tsabtacce sau bakwai.

7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.

8 Mugaye suna yawo a sake sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.

Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™

Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.

An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.

Hausa Contemporary Bible™

Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.

Used with permission. All rights reserved worldwide.

Biblica, Inc.
ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:



ကြော်ငြာတွေ