Zabura 113 - Sabon Rai Don Kowa 2020Zabura 113 1 Yabi Ubangiji. Ku yabe shi, ya ku bayin Ubangiji, ku yabi sunan Ubangiji. 2 Bari a yabi sunan Ubangiji, yanzu da har abada kuma. 3 Daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa, a yabi sunan Ubangiji. 4 Ana ɗaukaka Ubangiji a bisa dukan al’ummai, ɗaukakarsa a bisa sammai 5 Wane ne yake kamar Ubangiji Allahnmu, Wannan mai zama a kursiyi can bisa, 6 wanda yake sunkuya yă dubi sammai da duniya? 7 Yakan tā da matalauta daga ƙura yakan ɗaga mabukata daga tarin toka; 8 ya zaunar da su tare da sarakuna, tare da sarakunan mutanensu. 9 Yakan zaunar da matar da ba haihuwa a gidanta ta zama kamar mahaifiyar ’ya’ya mai farin ciki. Yabi Ubangiji. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.