2 Tarihi 27 - Sabon Rai Don Kowa 2020Yotam sarkin Yahuda ( 2 Sarakuna 15.32-38 ) 1 Yotam yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. Sunan mahaifiyarsa Yerusha, ’yar Zadok. 2 Ya yi abin da yake daidai a gaban Ubangiji, kamar yadda mahaifinsa Uzziya ya yi, sai dai bai kutsa cikin haikalin Ubangiji kamar mahaifinsa ba. Mutane kuwa, suka ci gaba da aikata ayyukan lalaci. 3 Yotam ya sāke ginin Ƙofar Bisa na haikalin Ubangiji, ya kuma yi aiki sosai a katanga a tudun Ofel. 4 Ya gina garuruwa a tuddan Yahuda, ya giggina katanga da gine-gine masu tsawo a wuraren da suke a kurmi. 5 Yotam ya yi yaƙi da sarkin Ammonawa ya kuma ci su. A wannan shekara Ammonawa suka biya shi haraji talenti ɗari na azurfa, garwan alkama dubu goma da kuma garwa dubu goma na sha’ir. Ammonawa suka kawo masa wannan kuma a shekara ta biyu da ta uku. 6 Yotam ya ƙaru a iko saboda ya daidaita al’amuransa a gaban Ubangiji Allahnsa. 7 Sauran ayyuka a mulkin Yotam, haɗe da dukan yaƙe-yaƙensa da waɗansu abubuwan da ya yi, suna a rubuce a littafin sarakunan Isra’ila da na Yahuda. 8 Yana da shekara ashirin da biyar sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi mulki a Urushalima shekara goma sha shida. 9 Yotam ya huta tare da kakanninsa, aka kuma binne shi a Birnin Dawuda. Sai Ahaz ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki. |
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.
Biblica, Inc.