Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -

Zabura 93 - Littafi Mai Tsarki


Allah Sarki Ne

1 Ubangiji sarki ne! Yana saye da ɗaukaka, suturarsa ƙarfi ne. Hakika duniya ta kahu sosai a inda take, Ba kuwa za ta jijjigu ba.

2 Kursiyinka, ya Ubangiji, ya kahu tun daga farko, Kana nan tun fil azal.

3 Ya Ubangiji, zurfafan teku suna ta da muryarsu, Suna ta da muryarsu da ruri.

4 Ubangiji yana mulki cikin Sama, Mulkinsa mafifici ne, Fiye da rurin teku, Fiye da ikon raƙuman ruwan teku.

5 Dokokinka dawwamammu ne, ya Ubangiji, Haikalinka kuwa tsattsarka ne ƙwarai, Har abada abadin.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:



ကြော်ငြာတွေ