Zabura 82 - Littafi Mai TsarkiTsautawa a kan Muguwar Shari'a 1 Allah yana matsayinsa a taron jama'arsa, Yakan zartar da nufinsa a taron alloli. 2 Tilas ku daina yin rashin gaskiya a shari'a, Ku daina goyon bayan mugaye! 3 Ku kāre hakkin talakawa da na marayu, Ku yi adalci ga matalauta, Da waɗanda ba su da mataimaki. 4 Ku kuɓutar da talakawa da matalauta, Ku cece su daga ikon mugaye! 5 “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye! Kuna zaune cikin duhu, Ga shi, ba adalci a duniya sam! 6 Na faɗa muku, ku alloli ne, Cewa dukanku 'ya'ya ne na Maɗaukaki. 7 Amma za ku mutu kamar kowane mutum, Ku fāɗi kamar kowane basarauce.” 8 Ya Allah, ka zo, ka mallaki duniya, Dukan al'ummai naka ne. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria