Zabura 75 - Littafi Mai TsarkiAllah Ya Ƙasƙantar da Mugaye, Ya Ɗaukaka Adalai 1 Muna yabonka, ya Allah, muna yabonka! Muna shelar sunanka mai girma, Muna kuwa faɗa abubuwan banmamaki da ka aikata! 2 “Na ƙayyade lokacin yin shari'a,” in ji Ubangiji Allah, “Zan kuwa yi shari'ar gaskiya. 3 Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace, Zan ƙarfafa harsashin gininta. 4 Na faɗa wa masu girmankai kada su yi taƙama, Na kuma faɗa wa mugaye kada su yi fāriya, 5 Na dai faɗa musu su daina yanga, Su daina yin taƙama.” 6 Hukunci ba daga gabas, ko yamma, Ko daga kudu, ko arewa yake zuwa ba. 7 Allah yake yin shari'a, Yana ƙasƙantar da waɗansu, ya kuma ɗaukaka waɗansu. 8 Ubangiji yana riƙe da ƙoƙo, Cike da sabon ruwan inabi mai ƙarfi, Yana zuba shi, dukan mugaye kuwa suna ta sha, Suka shanye shi ƙaƙaf. 9 Amma har abada ba zan daina yin magana a kan Allah na Yakubu ba, Ko in daina raira yabbai gare shi. 10 Shi zai karya ikon mugaye, Amma za a ƙara wa masu adalci ƙarfi. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria