Zabura 70 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Kuɓuta 1 Ka cece ni, ya Allah! Ya Ubangiji, ka yi hanzari ka taimake ni! 2 Ka sa masu so su kashe ni, A ci nasara a kansu, su ruɗe! Ka sa waɗanda suke murna saboda wahalaina, su koma baya, su sha kunya! 3 Ka sa waɗanda suke mini ba'a Su razana sabili da fāɗuwarsu! 4 Ka sa dukan waɗanda suke zuwa gare ka Su yi murna, su yi farin ciki! Ka sa waɗanda suke ƙaunar cetonka Kullayaumi su ce, “Allah da girma yake!” 5 Ba ni da ƙarfi, ba mataimaki, Ya Allah, ka zo wurina da hanzari. Kai ne mataimakina da Mai Cetona, Kada ka yi jinkiri, ya Ubangiji! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria