Zabura 67 - Littafi Mai TsarkiWaƙar Miƙa Hadaya ta Godiya 1 Ka yi mana jinƙai, ya Allah, ka sa mana albarka, Ka dube mu da idon rahama, 2 Domin dukan duniya ta san nufinka, Dukan sauran al'umma kuma su san cetonka. 3 Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah, Da ma dukan mutane su yabe ka! 4 Da ma sauran al'umma su yi murna, su raira waƙa ta farin ciki, Domin kana yi wa jama'a shari'a ta adalci, Kana kuma bi da dukan sauran al'umma. 5 Da ma dukan mutane su yabe ka, ya Allah, Da ma dukan mutane su yabe ka! 6 Ƙasa ta ba da amfaninta, Allah, wanda yake Allahnmu ne, ya sa mana albarka. 7 Allah ya sa mana albarka, Da ma dukan jama'a ko'ina su girmama shi. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria