Zabura 64 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Tsari 1 Ina shan wahala, ya Allah, ka ji addu'ata! Ina jin tsoro, ka cece ni daga maƙiyana! 2 Ka kiyaye ni daga ƙulle-ƙullen mugaye, Da iskancin mugayen mutane. 3 Sukan wasa harsunansu kamar takuba, Sukan kai bāra da mugayen maganganu kamar kibau. 4 Sukan yi kwanto su harbi mutanen kirki da kibau, Nan da nan sukan yi harbi, ba su kuwa jin tsoro. 5 Suna ƙarfafa junansu cikin yin mugayen ƙulle-ƙullensu, Sukan yi ta taɗi a kan inda za su kafa tarkunansu. “Ba wanda zai gan mu,” in ji su. 6 Sukan shirya maƙarƙashiya, su ce, “Ai, mun gama shirin aikata laifi sarai.” Zuciyar mutum da tunaninsa, suna da wuyar ganewa! 7 Amma Allah zai harbe su da kibansa, Za a yi musu rauni nan da nan. 8 Zai hallaka su saboda maganganunsu, Duk wanda ya gan su zai kaɗa kansa. 9 Dukansu za su ji tsoro, Za su faɗi abin da Allah ya aikata, Su yi tunani a kan ayyukansa. 10 Dukan masu adalci za su yi murna, Saboda abin da Ubangiji ya aikata. Za su sami mafaka a gare shi, Dukan mutanen kirki za su yabe shi. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria