Zabura 52 - Littafi Mai TsarkiHukuncin Allah da Alherinsa 1 Me ya sa kake fariya da muguntarka, Ya kai, babban mutum? Ƙaunar Allah tana nan a koyaushe. 2 Kana shirya maƙarƙashiya don ka lalatar da waɗansu, Harshenka kamar aska mai kaifi yake. Kana ƙirƙiro ƙarairayi kullum. 3 Kana ƙaunar mugunta fiye da nagarta, Kana kuwa ƙaunar faɗar ƙarya fiye da gaskiya. 4 Kana jin daɗin cutar mutane da maganganunka, Ya kai, maƙaryaci! 5 Don haka Allah zai ɓata ka har abada, Zai kama ka, yă jawo ka daga alfarwarka, Zai kawar da kai daga ƙasar masu rai. 6 Adalai za su ga wannan, su ji tsoro, Za su yi maka dariya, su ce, 7 “Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah Don ya sami zaman lafiyarsa ba. A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa. Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.” 8 Amma ni, kamar itacen zaitun nake, wanda yake girma kusa da Haikalin Allah, Ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarsa har abada abadin. 9 Zan gode maka, ya Ubangiji, Saboda abin da ka aikata. Zan dogara gare ka, Sa'ad da nake sujada tare da jama'arka, Domin kai mai alheri ne. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria