Zabura 47 - Littafi Mai TsarkiAllah ne Mai Mulkin Duka 1 Ku yi tāfi saboda farin ciki, Ya ku jama'a duka! Ku raira waƙoƙi da karfi, ku yabi Allah! 2 A ji tsoron Ubangiji Mai Iko Dukka, Shi babban Sarki ne, ya mallaki dukan duniya. 3 Ya ba mu nasara a bisa jama'o'i, Ya sa muka yi mulkin al'ummai, 4 Ya zaɓar mana ƙasar da muke zaune, Wadda take mallaka ce ta fāriya, ta jama'arsa Wadda yake ƙauna. 5 Allah ya hau kan kursiyinsa! Aka yi ta sowa ta murna, ana ta busa ƙahoni, Lokacin da Ubangiji yake hawa! 6 Ku raira yabbai ga Allah, Ku raira yabbai ga sarkinmu! 7 Allah sarki ne na duniya duka, Ku yabe shi da waƙoƙi! 8 Allah yana zaune kan kursiyinsa mai tsarki, Yana mulkin al'ummai, 9 Masu mulkin al'ummai suka tattaru Tare da jama'ar Allah na Ibrahim. Allah shi ne garkuwar jarumawa, Yana mulkin duka! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria