Zabura 46 - Littafi Mai TsarkiAllah ne Mafakarmu da Ƙarfinmu 1 Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, Kullum a shirye yake yă yi taimako a lokacin wahala. 2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, Ko da duniya za ta girgiza, Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku, 3 Ko da a ce tekuna za su yi ruri su tumbatsa, Tuddai kuma su girgiza saboda tangaɗin tekun. 4 Akwai kogin da yake kawo farin ciki a birnin Allah, Da cikin tsattsarkan Haikali na Maɗaukaki. 5 Allah yana zaune cikin birnin, Ba kuwa za a hallaka birnin ba, faufau. Da asuba Allah zai kawo musu gudunmawa. 6 An kaɓantar da sauran al'umma, mulkoki suka girgiza, Allah ya yi tsawa, duniya kuwa ta narke. 7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu! 8 Zo ku ga abin da Ubangiji ya yi! Dubi irin ayyukan al'ajabi da ya yi a duniya! 9 Ya hana yaƙoƙi ko'ina a duniya, Yana karya bakkuna, yana lalatar da māsu, Yana ƙone karusai da wuta. 10 Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!” 11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu, Allah na Yakubu shi ne mafakarmu! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria