Zabura 4 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Maraice ta Dogara ga Allah 1 Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata! 2 Ku mutanen nan, sai yaushe za ku daina zagina? Sai yaushe za ku daina ƙaunar abubuwan banza, Da bin abin da yake na ƙarya? 3 Ku tuna fa, Ubangiji ne ya zaɓe ni domin in zama nasa, Ya kuma ji ni lokacin da na yi kira gare shi. 4 Ku ji tsoro, ku daina aikata zunubinku, Ku yi tunani da gaske a kan wannan A kaɗaice, shiru, a ɗakunanku. 5 Ku miƙa wa Ubangiji hadayun da suka dace, Ku kuma dogara gare shi. 6 Akwai mutane da yawa da suke cewa, “Da ma a sa mana albarka!” Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji! 7 Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne, Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi. 8 Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni, Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria