Zabura 28 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Roƙo da Yabo 1 Ina kira gare ka, ya Ubangiji mai kāre ni, Ka ji kukana! In kuwa ba ka amsa mini ba, Zan zama ɗaya daga cikin waɗanda suka gangara zuwa lahira. 2 Ka ji ni lokacin da na yi kuka gare ka neman taimako, Ina ɗaga hannuwana wajen tsattsarkan Haikalinka. 3 Kada ka kāshe ni tare da mugaye, Tare da masu aikata mugunta, Mutane waɗanda maganarsu kamar ta zumunci ce, Amma zukatansu cike suke da ƙiyayya. 4 Ka hukunta su saboda abin da suka aikata. Ka hukunta su saboda dukan ayyukansu, Ka ba su abin da ya cancance su! 5 Ba su kula da abin da Ubangiji ya yi ba, Ko kuma abin da ya halitta, Don haka zai hukunta su, ya hallaka su har abada. 6 A yabi Ubangiji, Gama ya ji kukana na neman taimako! 7 Ubangiji yakan kiyaye ni, yă tsare ni. Na dogara gare shi. Ya taimake ni, don haka ina murna, Ina raira masa waƙoƙin yabo. 8 Ubangiji yana kiyaye jama'arsa, Yakan kiyaye sarkinsa da ya zaɓa, ya kuma cece shi. 9 Ka ceci jama'arka, ya Ubangiji, Ka sa wa waɗanda suke naka albarka! Ka zama makiyayinsu, Ka lura da su har abada. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria