Zabura 24 - Littafi Mai TsarkiSarkin Ɗaukaka 1 Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne, Duniya da dukan mazaunanta nasa ne. 2 Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa, Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku. 3 Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji? Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka? 4 Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani, Wanda ba ya yi wa gumaka sujada, Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya. 5 Ubangiji zai sa masa albarka, Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi. 6 Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah, Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu. 7 A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo! 8 Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai nasara cikin yaƙi! 9 A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo! 10 Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria