Zabura 20 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Nasara 1 Ubangiji ya amsa maka a ranar wahala! Allah na Yakubu ya kiyaye ka! 2 Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa, Ya kawo maka gudunmawa daga Sihiyona. 3 Ya karɓi hadayunka, Ya kuma ji daɗin dukan sadakokinka. 4 Ya ba ka abin da kake bukata, Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara. 5 Mu kuma, sai mu yi sowa ta farin ciki saboda ka ci nasara, Mu yi bikin cin nasara da ka yi, Da yabon Ubangiji Allahnmu. Allah ya amsa dukan roƙe-roƙenka! 6 Yanzu dai na sani Ubangiji yakan ba da nasara ga zaɓaɓɓen sarkinsa, Yakan amsa masa daga samaniyarsa mai tsarki, Da ikonsa mai girma yakan sa shi yă yi nasara. 7 Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara, Waɗansu kuwa ga dawakansu, Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara! 8 Za su yi tuntuɓe su fāɗi, Amma mu za mu tashi mu tsaya daram! 9 Ka ba sarki nasara, ya Ubangiji, Ubangiji zai amsa mana sa'ad da muka yi kira. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria