Zabura 15 - Littafi Mai TsarkiMazauna a Tudun Allah Mai Tsarki 1 Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka? Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka? 2 Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, Yana kuwa aikata abin da yake daidai, Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya, 3 Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu. Ba ya zargin abokansa, Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa. 4 Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su, Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya, Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa, 5 Yana ba da rance ba ruwa, Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria