Zabura 137 - Littafi Mai TsarkiKukan Isra'ilawa a Baƙuwar Ƙasa 1 A bakin kogunan Babila Muka zauna muka yi ta kuka, Sa'ad da muka tuna da Sihiyona. 2 A rassan itatuwan wardi da suke kusa da mu Muka rataye garayunmu. 3 Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa, Suka ce mana, “Ku yi mana shagali Da waƙar da aka raira wa Sihiyona!” 4 Kaƙa za mu raira waƙar Ubangiji A baƙuwar ƙasa? 5 Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya, Idan na manta da ke, Urushalima! 6 Da ma kada in ƙara iya raira waƙa, Idan na manta da ke, Idan ban tuna ke ce Babbar abar farin ciki ba! 7 Ka tuna, ya Ubangiji, da abin da Edomawa suka yi, A ranar da aka ci Urushalima. Ka tuna da yadda suka ce, “A ragargaza ta har ƙasa!” 8 Babila, za a hallaka ki! Mai farin ciki ne shi wanda ya sāka miki Bisa ga abin da kika yi mana. 9 Mai farin ciki ne shi wanda zai kwashi jariranki Yă fyaɗa su a kan duwatsu! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria