Kira a Yabi Allah 1 Ku zo mu yabi Ubangiji, Dukanku bayinsa, Dukanku waɗanda kuke yi masa hidima, A cikin Haikalinsa da dare.
2 Ku ɗaga hannuwanku sama, ku yi addu'a a Haikali, Ku yabi Ubangiji!
3 Ubangiji wanda ya yi sama da duniya, Ya sa muku albarka daga Sihiyona.