Zabura 133 - Littafi Mai TsarkiYaba Ƙaunar 'Yan'uwanci 1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa! 2 Yana kama da man zaitun mai daraja, Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa, Har zuwa wuyan riganunsa. 3 Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon, Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona. A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa, Rai na har abada. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria