Zabura 131 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Tawali'u 1 'Ya Ubangiji, na rabu da girmankai, Na bar yin fariya, Ba ruwana da manyan al'amura, Ba ruwana kuma da zantuttukan da suka fi ƙarfina. 2 Amma na haƙura, raina a kwance, Kamar jinjirin da yake kwance jalisan a hannun mahaifiyarsa, Haka zuciyata take kwance. 3 Ya Isra'ila, ka dogara ga Ubangiji, Daga yanzu har abada! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria