Zabura 13 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Taimako daga Wahala 1 Har yaushe za ka manta da ni, ya Ubangiji? Har abada ne? Har yaushe za ka ɓoye mini fuskarka? 2 Har yaushe raina zai jure da shan wahala? Har yaushe zan yi ta ɓacin rai dare da rana? Har yaushe maƙiyana za su riƙa cin nasara a kaina? 3 Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini, Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu. 4 Sa'an nan maƙiyana ba za su ce, “Ai, mun yi nasara da shi” ba! Ba za su iya yin murna saboda fāɗuwata ba. 5 Amma ina dogara ga madawwamiyar ƙaunarka, Zan yi murna gama za ka cece ni. 6 Zan raira waƙa ga Ubangiji, Gama ya kyautata mini. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria