Zabura 129 - Littafi Mai TsarkiAddu'a a kan Maƙiyan Isra'ila 1 Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntar Da maƙiyanka suka tsananta maka da ita, Tun kana ƙarami! 2 “Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta, Tun ina ƙarami, Amma ba su yi nasara da ni ba. 3 Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana, Suka mai da shi kamar gonar da aka nome. 4 Amma Ubangiji mai adalci, Ya 'yantar da ni daga bauta.” 5 Allah ya sa duk waɗanda suke ƙin Sihiyona, A yi nasara da su a kuma kore su! 6 Allah ya sa su zama kamar ciyawar da take girma a kan soraye, Ta kuwa bushe kafin ta isa yanka. 7 Ba wanda zai tattara ta, Ya ɗaure ta dami dami. 8 Duk waɗanda suke wucewa a hanya ba za su ce, “Ubangiji ya sa maka albarka!” ba, Ko su ce, “Muna sa maka albarka da sunan Ubangiji!” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria