Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -

Zabura 127 - Littafi Mai Tsarki


Yabon Alherin Ubangiji

1 Idan ba Ubangiji ne ya gina gidan ba, Aikin magina banza ne. Idan ba Ubangiji ne ya tsare birnin ba, Ba wani amfani a sa matsara su yi tsaro.

2 Ba wani amfani a sha wahalar aiki saboda abinci, A yi asubancin tashi, a yi makarar kwanciya, Gama Ubangiji yakan hutar da waɗanda yake ƙauna.

3 'Ya'ya kyauta ne daga wurin Ubangiji, Albarka ce ta musamman.

4 'Ya'ya maza da mutum ya haifa a lokacin ƙuruciyarsa Kamar kibau suke a hannun mayaƙi.

5 Mai farin ciki ne mutumin da yake da irin waɗannan kibau da yawa! Faufau ba za a ci nasara a kansa ba, Sa'ad da ya kara da maƙiyansa a wurin shari'a.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:



ကြော်ငြာတွေ