Zabura 125 - Littafi Mai TsarkiZaman Lafiyar Jama'ar Allah 1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba. 2 Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima, Haka nan Ubangiji zai kewaye jama'arsa, Daga yanzu har abada. 3 Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba, Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi. 4 Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri, Su waɗanda suke biyayya da umarnanka! 5 Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu, Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta! Salama ta kasance tare da Isra'ila! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria