Zabura 124 - Littafi Mai TsarkiAllah Ne Mai Ceton Jama'arsa 1 Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, Da me zai faru? Ba da amsa, ya Isra'ila! 2 “Da a ce Ubangiji ba ya tare da mu, A lokacin da abokan gābanmu suka auka mana, 3 Da sun haɗiye mu da rai a lokacin nan, Saboda zafin fushi da suke yi da mu, 4 Da rigyawa ta kwashe mu, Da ruwa yi ci mu, 5 Kwararowar ruwa ya nutsar da mu.” 6 Sai mu gode wa Ubangiji, Da bai bar abokan gābanmu su hallaka mu ba. 7 Mun kuɓuta kamar tsuntsu daga tarkon mai farauta, Tarkon ya tsinke, mun 'yantu! 8 Taimakonmu daga wurin Ubangiji yake zuwa, Shi wanda ya yi sama da duniya. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria