Zabura 123 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Jinƙai 1 Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka, A Sama inda kake mulki. 2 Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa, Baranya kuma ga uwargijiyarta, Haka nan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu, Har mu sami jinƙanka. 3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, An gwada mana wulakanci matuƙa! 4 Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a, Azzalumai masu girmankai sun raina mu! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria