Zabura 122 - Littafi Mai TsarkiYabon Urushalima 1 Na yi murna sa'ad da suka ce mini, “Tashi mu tafi Haikalin Ubangiji!” 2 Ga shi kuwa, mun iso, Muna tsaye a ƙofofin Urushalima! 3 Urushalima birni ce wadda aka maido ta yadda take dā, Da kyakkyawan tsari, a shirye! 4 A nan kabilai sukan zo, Kabilan Isra'ila, Domin su yi godiya ga Ubangiji, Kamar yadda ya umarce su. 5 A nan majalisu suke, Wurin da sarki yake yi wa jama'arsa shari'a. 6 Ku yi wa Urushalima addu'ar salama! “Allah ya sa masu ƙaunarki su arzuta! 7 Salama ta samu a garukanki, Da zaman lafiya kuma a fādodinki.” 8 Saboda abokaina da aminaina, Na ce wa Urushalima, “Salama a gare ki!” 9 Saboda Haikalin Ubangiji, Allahnmu, Ina addu'a domin ki arzuta. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria