Zabura 121 - Littafi Mai TsarkiUbangiji Ne Yake Kiyaye Ku 1 Na duba wajen duwatsu, Daga ina taimakona zai zo? 2 Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji, Wanda ya yi sama da ƙasa. 3 Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba! 4 Makiyayin Isra'ila, Ba ya gyangyaɗi ko barci! 5 Ubangiji zai lura da kai, Yana kusa da kai domin ya kiyaye ka. 6 Ba za ka sha rana ba, Ko farin wata da dare. 7 Ubangiji zai kiyaye ka daga dukan hatsari, Zai sa ka zauna lafiya. 8 Zai kiyaye shigarka da fitarka, Tun daga yanzu har abada. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria