Zabura 120 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Taimako 1 Sa'ad da nake shan wahala, Na yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa amsa mini. 2 Ka cece ni, ya Ubangiji, Daga maƙaryata da masu ruɗi! 3 Ku maƙaryata, me Allah zai yi da ku? Yaya zai hukunta ku? 4 Da kibau masu tsini na mayaƙa, Da garwashin wuta zai hukunta ku! 5 Zama tare da ku mugun abu ne, kamar zama a Meshek, Ko tare da mutanen Kedar! 6 Na daɗe ƙwarai ina zama tare da mutane marasa son salama! 7 Sa'ad da nake maganar salama, Su sai su yi ta yaƙi. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria