1 Ku yabi Ubangiji, ku dukan sauran al'ummai! Ku yabe shi, ku dukan kabilai!
2 Madawwamiyar ƙaunarsa, da ƙarfi take, Amincinsa kuma tabbatacce ne har abada. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!
@Bible Society of Nigeria 1979