Zabura 113 - Littafi Mai TsarkiYabon Alherin Ubangiji 1 Yabo Ya tabbata ga Ubangiji! Ku bayin Ubangiji, Ku yabi sunansa! 2 Za a yabi sunansa yanzu da har abada! 3 Daga gabas zuwa yamma a yabi sunan Ubangiji! 4 Ubangiji yake mulkin dukan sauran al'umma, Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai. 5 Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu. Yana zaune a can ƙwanƙolin sama, 6 Amma ya duba ƙasa, Ya dubi sammai da duniya. 7 Yakan ɗaga talakawa daga ƙura, Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu. 8 Yakan sa su zama abokan sarakuna, Sarakunan jama'arsa. 9 Yakan girmama matar da ba ta haihuwa a gidanta, Yakan sa ta yi farin ciki ta wurin ba ta 'ya'ya. Yabo ya tabbata ga Ubangiji! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria