Zabura 100 - Littafi Mai TsarkiWaƙar Yabo 1 Bari dukan duniya ta raira waƙar farin ciki ga Ubangiji! 2 Ku yi wa Ubangiji sujada da murna, Ku zo gabansa, kuna raira waƙoƙin farin ciki! 3 Kada fa a manta da cewa, Ubangiji shi ne Allah! Shi ne ya yi mu, mu kuwa nasa ne, Mu jama'arsa ne, mu garkensa ne. 4 Ku shiga Haikalinsa da godiya, Ku shiga wurinsa mai tsarki, ku yabe shi! Ku gode masa, ku yabe shi! 5 Ubangiji nagari ne, Ƙaunarsa madawwamiya ce, Amincinsa kuwa har abada abadin ne. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria