Mika 3 - Littafi Mai TsarkiAn Yi wa Shugabannin Isra'ila Faɗa 1 Ni kuwa na ce, “Ku ji, ya ku shugabannin mutanen Yakubu, Da ku sarakunan Isra'ila. Ya kamata ku san shari'a. 2 Amma kuna ƙin nagarta, kuna ƙaunar mugunta, Kuna feɗe mutanena, Kuna kuma fizge naman jikinsu daga ƙasusuwansu. 3 Kuna cin naman mutanena, kuna feɗe fatar jikinsu, Kuna kakkarya ƙasusuwansu, Kuna yanyanka su gunduwa gunduwa kamar naman da za a sa a tukunya.” 4 Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji, Amma Ubangiji ba zai amsa musu ba. Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan lokaci, Saboda mugayen ayyukansu. 5 Ga abin da Ubangiji ya ce a kan annabawan da suka bi da mutanensa a karkace, Waɗanda suke cewa, “Salama,” sa'ad da suke da abinci, Amma sukan kai yaƙin shahada Ga wanda bai ba su abin sawa a baka ba. 6 Saboda haka kome zai zama dare da duhu, ba wahayi ko duba. Rana za ta fāɗi a kan annabawa, Yini zai zama musu duhu baƙi ƙirin. 7 Masu gani za su sha kunya, Masu duba kuwa za su ruɗe, Dukansu za su rufe bakinsu, Gama ba amsa daga wurin Allah. 8 Amma ni ina cike da iko, Da Ruhun Ubangiji, Da shari'a da ƙarfin hali, Don in sanar wa Yakubu da laifinsa, Isra'ila kuma da zunubinsa. 9 Ku ji wannan, ya ku shugabannin jama'ar Yakubu, Da ku sarakunan mutanen Isra'ila, Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya, Kuna karkatar da dukan gaskiya. 10 Kuna gina Sihiyona da jini, Kuna kuwa gina Urushalima da zalunci. 11 Shari'ar shugabannin ƙasar ta cin hanci ce. Firistocinta suna koyarwa don neman riba, Haka kuma annabawa suna annabci don neman kuɗi. Duk da haka suna dogara ga Ubangiji, suna cewa, “Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu, Ba masifar da za ta same mu.” 12 Saboda ku kuwa za a nome Sihiyona kamar gona, Urushalima kuwa za ta zama tsibin kufai, Dutse inda Haikali yake zai zama kurmi. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria