Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -

Ibraniyawa 7 - Littafi Mai Tsarki


Firist Kwatancin Malkisadik

1 Shi wannan Malkisadik, Sarkin Urushalima, firist na Allah Maɗaukaki, ya gamu da Ibrahim a lokacin da Ibrahim yake dawowa daga kisan sarakuna, ya sa masa albarka.

2 Shi ne kuwa Ibrahim ya ba shi ushirin kome. Da farko dai, kamar yadda ma'anar sunansa take, shi sarkin adalci ne, sa'an nan kuma Sarkin Urushalima ne, wato, sarkin salama.

3 Shi ba shi da uwa ko uba, ba a kuma san asalinsa ba. Ba shi da ranar haihuwa balle ranar mutuwa, yana dai kama da Ɗan Allah, firist ne har abada.

4 Kai, ku dubi irin girmansa! Har kakanmu Ibrahim ma ya ba shi ushirin ganima!

5 Ga shi kuma, waɗansu na zuriyar Lawi, in sun sami matsayin firist, akan umarce su bisa ga Shari'a su karɓi ushiri a gun jama'a, wato a gun 'yan'uwansu, ko da yake su ma zuriyar Ibrahim ne.

6 Amma wannan, wanda ma ba a asalin Lawi yake ba, ya karɓi ushiri a gun Ibrahim, har ya sa masa albarka, shi ma da aka yi wa alkawarai.

7 Ai, ba abin musu ba ne, cewa na gaba shi yake sa wa na baya albarka.

8 Ga shi, a nan masu karɓar ushiri, mutane ne masu mutuwa, a can kuwa mai karɓar wanda aka shaida shi, rayayye ne.

9 A ma iya cewa ko Lawi ma da kansa, mai karɓar ushiri, ya ba da ushiri ta wurin Ibrahim,

10 don shi Lawi yana daga tsatson kakansa Ibrahim, sa'ad da Ibrahim ɗin ya gamu da Malkisadik.

11 Gama da a ce kammala tana samuwa ta wurin firistoci na zuriyar Lawi (don ta gare su ne jama'a suka karɓi shari'a), wace bukata kuma ake da ita ta wani firist dabam ya bayyana kwatancin ɗabi'ar Malkisadik, wanda za a ambata ba kwatancin ɗabi'ar Haruna ba?

12 Domin in an sauya matsayin firistoci, sai tilas a sauya Shari'a kuma.

13 Domin kuwa shi wannan da aka faɗi waɗannan abubuwa a game da shi, ai, na wata kabila ne dabam, wadda ba waninta da ya taɓa hidimar bagadin hadaya.

14 Tabbatacce ne, cewa Ubangijinmu ya fito daga zuriyar Yahuza ne, Musa kuwa bai ce kome ba a game da kabilar nan a kan zancen firistoci.

15 Wannan kuma ya ƙara fitowa fili sosai, sa'ad da wani firist dabam ya bayyana kamar Malkisadik,

16 wanda kuwa ya zama firist, ba bisa ga wata ka'ida ta al'adar 'yan adam ba, sai dai ta wurin ikon rai marar gushewa.

17 Domin an shaide shi da cewa, “Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”

18 Ta wani hali an soke wani umarni ta dā saboda rauninsa da kuma rashin amfaninsa,

19 don Shari'a ba ta kammala kome ba, ta wani hali kuma an shigo da wani bege wanda yake mafi kyau, ta wurinsa kuwa muke kusatar Allah.

20 Ba kuwa da rashin rantsuwa aka yi haka ba.

21 Waɗancan sun zama firistoci, ba tare da an yi musu rantsuwa ba, amma wannan kam, sai da aka yi masa rantsuwa, da Allah ya ce masa, “Ubangiji ya rantse, Ba kuwa zai ta da maganarsa ba cewa, ‘Kai firist ne har abada.’ ”

22 A sanadin wannan ne Yesu ya zama lamunin alkawarin da ya fi wancan nesa.

23 Waɗancan firistoci, an yi su da yawa, domin mutuwa ta hana su tabbata a aikin.

24 Amma shi da yake madawwami ne, yana da matsayinsa na firist wanda ba ya komawa hannun wani.

25 Saboda haka, yana da ikon ceton masu kusatowa ga Allah ta wurinsa, matuƙar ceto, tun da yake kullum a raye yake saboda yi musu addu'a.

26 Irin babban firist wanda muke bukata ke nan, mai tsarki, marar aibu, marar cikas, keɓaɓɓe daga masu zunubi, ɗaukakke kuma birbishin sammai.

27 Ba zai miƙa hadaya kowace rana kumar waɗancan manyan firistocin ba, wato, da farko saboda zunubansa, sa'an nan kuma saboda na jama'a. Wannan ya yi ta ne sau ɗaya tak, lokacin da ya miƙa kansa hadaya.

28 Wato shari'a tana sa mutane su zama manyan firistoci duk da rauninsu, amma maganar nan ta rantsuwa da ta sauko bayan Shari'a, ta sa Ɗa wanda yake kammalalle har abada.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:



ကြော်ငြာတွေ