Ibraniyawa 11 - Littafi Mai TsarkiBangaskiya 1 To, bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar abubuwan da ake bege, a kai, ita ce kuma tabbatawar abubuwan da ba a gani ba. 2 Domin ta gare ta ne shugabannin dā suka sami yardar Allah. 3 Ta wurin bangaskiya muka fahimta, cewa ta faɗar Allah ce aka tsara duniya, har ma abubuwan da ake gani, daga abubuwan da ba a gani ne, suka kasance. 4 Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan Kayinu, ta wurin wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta wurin bangaskiyar nan tasa har ya zuwa yanzu yana magana. 5 Saboda bangaskiya ce aka ɗauke Anuhu, shi ya sa bai mutu ba, ba a kuwa same shi ba, domin Allah ya ɗauke shi. Tun kafin a ɗauke shi ma, an shaide shi a kan ya faranta wa Allah rai. 6 In ba a game da bangaskiya ba kuwa, ba shi yiwuwa a faranta masa rai. Domin duk wanda zai kusaci Allah, lalle ne ya gaskata cewa, akwai shi, yana kuma sakamako ga masu nemansa. 7 Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya. 8 Ta wurin bangaskiya Ibrahim ya yi biyayya, sa'ad da aka kira shi ya fita zuwa wata ƙasa da zai karɓa gādo. Ya kuwa fita, bai ma san inda za shi ba. 9 Ta wurin bangaskiya kuma ya yi baƙunci a ƙasar alkawari, kamar dai a ƙasar bare, suna zaune a cikin alfarwai, shi da Ishaku da Yakubu, abokan tarayya ga gādon alkawarin nan. 10 Yana ta jiran birnin nan mai tushe, wanda mai fasalta shi, mai gina shi kuma, Allah ne. 11 Ta wurin bangaskiya Saratu da kanta ta sami ikon yin ciki, ko da yake ta wuce lokacin haihuwa, tun da dai ta amince, cewa shi mai yin alkawarin nan amintacce ne. 12 Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurari, kamar yashi kuma dangam a bakin teku. 13 Waɗannan duka sun mutu cikin bangaskiyarsu, ba su kuwa sami abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkato su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda su baƙi ne, bare kuma a duniya. 14 Mutane masu irin wannan magana, ai, sun bayyana a fili, suna neman wata ƙasa ta kansu ne. 15 Da suna marmarin ƙasar nan da suka baro ne, da sun sami damar komawa. 16 Amma bisa ga hakika sun ɗokanta ne a kan wata ƙasa mafi kyau, wato ta Sama. Saboda haka ne, Allah ba ya jin kunya a ce da shi Allahnsu, don kuwa ya shirya musu birni. 17 Ta wurin bangaskiya Ibrahim, sa'ad da aka gwada shi, ya miƙa Ishaku hadaya, wato shi da ya yi na'am da alkawaran nan, ya yi shirin miƙa makaɗaicin ɗansa, 18 wanda a kansa aka yi faɗi cewa, “Ta wurin Ishaku ne za a lasafta zuriyarka.” 19 Ya amince da cewa, ko daga matattu Allah yana da iko yă ta da mutum. Ai kuwa, bisa ga misali, sai a ce daga matattu ne ya sāke samun Ishaku. 20 Ta wurin bangaskiya Ishaku ya sa wa Yakubu da Isuwa albarka a kan al'amuran da za su zo. 21 Ta wurin bangaskiya Yakubu, sa'ad da yake bakin mutuwa, ya sa wa 'ya'yan Yusufu albarka dukkansu biyu, ya kuma yi sujada, yana sunkuye a kan sandarsa. 22 Ta wurin bangaskiya Yusufu, da ajalinsa ya yi, ya yi maganar ƙaurar Isra'ilawa, har ya yi wasiyya a game da ƙasusuwansa. 23 Ta wurin bangaskiya ne, sa'ad da aka haifi Musa, iyayensa suka ɓoye shi har wata uku, domin sun ga yaron kyakkyawa ne, ba su kuma ji tsoron umarnin sarki ba. 24 Ta wurin bangaskiya Musa, sa'ad da ya girma, ya ƙi yarda a kira shi ɗan 'yar Fir'auna, 25 ya gwammaci ya jure shan wuya tare da jama'ar Allah, da ya mori romon zunubi, mai saurin wucewa. 26 Ya amince, cewa wulakanci saboda Almasihu wadata ce a gare shi, fiye da dukiyar ƙasar Masar, domin ya sa ido a kan sakamakon. 27 Ta wurin bangaskiya ya bar Masar, bai ji tsoron fushin sarki ba, ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa. 28 Ta wurin bangaskiya ya ci Jibin Ƙetarewa, ya yayyafa jini, domin kada mai hallakar da 'ya'yan fari ya taɓa Isra'ilawa. 29 Ta wurin bangaskiya suka haye Bahar Maliya ta busasshiyar ƙasa, amma da Masarawa suka yi ƙoƙarin yin haka, sai aka dulmuyar da su. 30 Ta wurin bangaskiya garun Yariko ya rushe, bayan an yi ta kewaya shi har kwana bakwai. 31 Ta wurin bangaskiya Rahab karuwar nan ba ta hallaka tare da maƙiya biyayya ba, ta karɓi 'yan ganganimar nan kamar aminai. 32 Me kuma zan ƙara cewa? Ai, lokaci zai ƙure mini a wajen ba da labarin su Gidiyon, da Barak, da Samson, da Yefta, da Dawuda, da Sama'ila, da kuma sauran annabawa, 33 waɗanda ta wurin bangaskiya suka ci masarautai, suka aikata adalci, suka sami cikar alkawarai, suka rurrufe bakunan zakoki, 34 suka i, wa ikon wuta, suka tsere wa kaifin takobi, suna marasa ƙarfi sai suka zama masu ƙarfi, suka yi jaruntaka a wajen yaƙi, suka fatattaka rundunar waɗansu ƙasashe. 35 Aka mayar wa mata da matattunsa da aka tasar. Waɗansu mutane kuma an azabta su har suka mutu, amma sun ƙi yarda da irin 'yancin da za a ba su, domin a tashe su su rayu da rayuwa mafi kyau. 36 Har wa yau kuma, waɗansu suka sha ba'a da bulala, har ma da ɗauri da jefawa a cikin kurkuku. 37 Aka jejeffe su da duwatsu, an gwada su, aka raba su biyu da zarto, aka sare su da takobi. Sun yi yawo saye da buzun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, da ƙunci, da wulakanci. 38 Su kam, duniya ba ta ma cancanci su zama a cikinta ba. Sun yi yawo a jazza da a kan duwatsu, suna kwana a cikin kogwanni da ramummuka. 39 Waɗannan duka, ko da yake Allah ya shaide su saboda bangaskiyarsu, duk da haka, ba su sami cikar alkawarin ba, 40 tun da Allah ya shirya mana wani abu mafi kyau, sai kuwa tare da mu ne za a kammala su. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria