Farawa 49 - Littafi Mai TsarkiFaɗar Yakubu a kan 'Ya'yansa 1 Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa: 2 “Ku taru ku ji, ya ku 'ya'yan Yakubu, maza, Ku kuma kasa kunne ga Isra'ila mahaifinku. 3 “Ra'ubainu, kai ɗan farina ne, ƙarfina, Ɗan balagata, isasshe kuma, mafi ƙarfi duka cikin 'ya'yana. 4 Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi. 5 “Saminu da Lawi 'yan'uwa ne, Suka mori takubansu cikin ta da hankali. 6 Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba, Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu ba, Gama cikin fushinsu suka kashe mutane, Cikin gangancinsu kuma suka gurgunta bijimai. 7 La'ananne ne fushinsu domin mai tsanani ne, Da hasalarsu kuma, gama bala'i ce. Zan warwatsa su cikin dukan ƙasar Yakubu, In ɗaiɗaitar su su cikin Isra'ilawa. 8 “Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka. 9 Yahuza ɗan zaki ne, Ya kashe ganima sa'an nan ya komo wurin ɓuyarsa. Yahuza kamar zaki yake, Yakan kwanta a miƙe, Ba mai ƙarfin halin da zai tsokane shi. 10 Yana riƙe da sandan mulkinsa, Ya sa shi a tsakanin ƙafafunsa, Har Shilo ya zo. Zai mallaki dukan jama'o'i. 11 Zai ɗaure aholakinsa a kurangar inabi, A kuranga mafi kyau, Zai wanke tufafinsa da ruwan inabi, Ruwan inabi ja wur kamar jini. 12 Idanunsa za su yi ja wur saboda shan ruwan inabi, Haƙoransa kuma su yi fari fat saboda shan madara. 13 “Zabaluna zai zauna a gefen teku, Zai zama tashar jiragen ruwa, Kan iyakarsa kuma zai kai har Sidon. 14 “Issaka alfadari ne ƙaƙƙarfa, Ya kwanta a miƙe tsakanin jakunkunan shimfiɗa. 15 Saboda ya ga wurin hutawa ne mai kyau, Ƙasar kuma mai kyau ce, Sai ya sunkuyar da kafaɗunsa domin ɗaukar kaya, Ya zama bawa, yana yin aiki mai wuya. 16 “Dan zai zama mai mulki ga mutanensa Kamar ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila. 17 Dan zai zama maciji a gefen hanya, Zai zama kububuwa a gefen turba, Mai saran diddigen doki Don mahayin ya fāɗi da baya. 18 Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji. 19 “Gad, 'yan fashi za su kai masa hari, Shi kuwa zai runtume su. 20 “Ashiru, ƙasarsa za ta ba da amfani mai yawa, Zai kuma yi tanadin abincin da ya dace da sarki. 21 “Naftali sakakkiyar barewa ce, Mai haihuwar kyawawan 'ya'ya. 22 “Yusufu jakin jeji ne, Jakin jeji a gefen maɓuɓɓuga Aholakan jeji a gefen tuddai. 23 Maharba suka tasar masa ba tausayi Suka fafare shi da kwari da baka. 24 Duk da haka bakunansu sun kakkarye. Damatsansu sun yayyage Ta wurin ikon Allah Mai Girma na Yakubu, Makiyayi, Dutse na Isra'ila. 25 Ta wurin Allah na mahaifinka wanda zai taimake ka, Ta wurin Allah Mai Iko Dukka wanda zai sa maka albarka Albarkun ruwan sama daga bisa, Da na zurfafa daga ƙarƙashin ƙasa, Da albarkun mama da na mahaifa. 26 Albarkun hatsi da na gari Albarkun daɗaɗɗun duwatsu, Abubuwan jin daɗi na madawwaman tuddai, Allah ya sa su zauna a kan Yusufu, Da a goshin wanda aka raba shi da 'yan'uwansa. 27 “Biliyaminu kyarkeci ne mai kisa, Da safe yakan cinye abin da ya kaso, Da maraice kuma yakan raba abin da ya kamo.” 28 Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi. Rasuwar Yakubu da Jana'izarsa 29 Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte, 30 a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta. 31 A can aka binne Ibrahim da Saratu matarsa. A can kuma suka binne Ishaku da Rifkatu matarsa. A can kuma na binne Lai'atu. 32 Da saurar da kogon da yake cikinta, an saye su daga Hittiyawa.” 33 Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria