1 Tarihi 25 - Littafi Mai TsarkiƘungiyoyin Mawaƙa 1 Dawuda fa da shugabannin Lawiyawa suka zaɓi waɗansu daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, da na Heman, da na Yedutun domin su raira waƙa da garayu, da molaye, da kuge. Ga waɗanda suka yi wannan hidima. 2 Daga cikin 'ya'yan Asaf, maza, Zakkur, da Yusufu, da Netaniya, da Asharela, Asaf mahaifinsu ne yake bi da su, shi ne kuma mawaƙin sarki. 3 Na wajen Yedutun, su ne 'ya'yan Yedutun, maza, wato Gedaliya, da Zeri, da Yeshaya, da Shimai, da Hashabiya, da Mattitiya, su shida ne. Mahaifinsu Yedutun shi ne yake bi da su, shi ne kuma mai raira waƙoƙi da garaya domin godiya da yabon Ubangiji. 4 Na wajen Heman, su ne 'ya'yan Heman, maza, wato Bukkiya, da Mattaniya, da Uzziyel, da Shebuwel, da Yerimot, da Hananiya, da Hanani, da Eliyata, da Giddalti, da Romamti-yezer, da Yoshbekasha, da Malloti, da Hotir, da Mahaziyot. 5 Allah ya ba Heman, wato annabin sarki, 'ya'ya maza su goma sha huɗu, da 'ya'ya mata su uku, kamar yadda ya yi alkawari, domin ya ba Heman iko. 6 Dukansu tsohonsu ne yake bi da su da raira waƙoƙi, da kaɗa kuge, da molaye da garayu, cikin Haikalin Ubangiji, domin yin sujada. Asaf, da Yedutun, da Heman suna ƙarƙashin umarnin sarki. 7 Jimillar horarrun mawaƙa don raira waƙa ga Ubangiji, su da 'yan'uwansu, duka waɗanda suke ƙwararru, su ɗari biyu da tamanin da takwas ne. 8 Sai suka jefa kuri'a domin su ba kowa aikin da zai yi, yaro da babba, malami da almajiri. 9-31 Waɗannan su ne shugabannin ƙungiyoyi ashirin da huɗu, na goma sha biyu biyu, bisa ga yadda aka tsara su ga aikin: 1. Yusufu daga iyalin Asaf 2. Gedaliya 3. Zakku 4. Zeri 5. Netaniya 6. Bukkiya 7. Asharela 8. Yeshaya 9. Mattaniya 10. Shimai 11. Uzziyel 12. Hashabiya 13. Shebuwel 14. Mattitiya 15. Yeremot 16. Hananiya 17. Yoshbekasha 18. Hanani 19. Malloti 20. Eliyata 21. Hotir 22. Giddalti 23. Mahaziyot 24. Romamtiyezer |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria