Zakariya 8:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Zan koma Sihiyona in zauna a Urushalima. Sa’an nan za a kira Urushalima Birnin Gaskiya, a kuma kira dutsen Ubangiji Maɗaukaki Dutse Mai Tsarki.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki3 Zan koma wurin Sihiyona, in zauna a tsakiyar Urushalima. Za a ce da Urushalima birnin gaskiya, da kuma dutsen Ubangiji Mai Runduna, tsattsarkan dutse. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Za su kuma dawo da dukan ’yan’uwanku, daga dukan al’ummai, zuwa dutsena mai tsarki a Urushalima kamar hadaya ga Ubangiji, a kan dawakai, a kekunan yaƙi da wagonu, da kuma a kan alfadarai da kuma raƙuma,” in ji Ubangiji. “Za su kawo su, kamar yadda Isra’ilawa suke kawo hadayun hatsi, zuwa haikalin Ubangiji a cikin tsabtatattun kore.