Zakariya 7:10 - Sabon Rai Don Kowa 202010 Kada ku danne gwauruwa ko maraya, baƙo ko talaka. A cikin zuciyarku kada ku yi mugun tunani game da juna.’ အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki10 Kada kuma ku zalunci gwauruwa, wato wadda mijinta ya rasu, da maraya, da baƙo, da matalauci, kada kuma waninku ya shirya wa ɗan'uwansa mugunta a zuciyarsa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.