Zakariya 5:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki4 Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Ta haka zan zo kusa da ku don in yi hukunci. Zan hanzarta ba da shaida a kan masu yin sihiri, da mazinata da masu shaidar zur. Zan ba da shaida a kan waɗanda suke zaluntar ma’aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye da marayu, suna kuma hana baƙi samun adalci, ba sa ma tsorona,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.