Zakariya 4:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Sai ya ce mini, “Wannan ce maganar Ubangiji ga Zerubbabel. ‘Ba ta wurin ƙarfi ba, ko ta wurin iko, sai dai ta wurin Ruhuna,’ in ji Ubangiji Maɗaukaki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki6 Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Asa ya kira ga Ubangiji Allahnsa ya ce, “Ubangiji, babu wani kamar ka da zai taimaki marar ƙarfi a kan mai ƙarfi. Ka taimake mu, ya Ubangiji Allahnmu, gama mun dogara a gare ka, kuma a cikin sunanka muka fito don mu yaƙi wannan babbar runduna. Ya Ubangiji, kai ne Allahnmu; kada ka bar mutum yă yi nasara a kanka.”