Zakariya 14:5 - Sabon Rai Don Kowa 20205 Za ku gudu ta wajen kwarin dutsena, gama zai miƙe har zuwa Azel. Za ku gudu kamar yadda kuka guje wa girgizar ƙasa a kwanakin Uzziya sarkin Yahuda. Sa’an nan Ubangiji Allahna zai zo, tare da duk masu tsarki. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Littafi Mai Tsarki5 Za ku gudu zuwa kwarin duwatsuna, gama kwarin duwatsu zai kai har Azel, kamar yadda kakanninku suka gudu a zamanin Azariya, Sarkin Yahuza, a lokacin da aka yi girgizar ƙasa. Sa'an nan Ubangiji Allahna zai zo tare da dukan tsarkakansa! အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.